Gwamnonin Najeriya sun ce ba za su iya biyan mafi ƙarancin albashi na ₦60,000 ba
Daga Abdullahi I. Adam
A daidai lokacin da ake sa ran jin sanarwar sabon mafi ƙarancin albashi wanda ake sa ran zai haura naira dubu sittin, kwatsam sai ga wata sanarwa daga ƙungiyar gwamnonin Najeriya inda su ka ce atafau su ba za su ma iya biyan naira dubu sittin a matsayin albashi mafi ƙaranci a jihohin nasu ba.
Gwamnonin sun ce kwata-kwata ba abu ne mai yiwuwa ba a wajensu, sannan kasada ne amincewa da naira dubu sittin ɗin domin ba za ta ɗore ba.
Bayanan gwamnonin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktar Sadarwa da Hulɗa da Jama’a ta Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF), Hajiya Halimah Salihu Ahmed ta fitar a jiya Juma’a wadda kuma tuni ƙungiyar gwamnonin ta wallafa ƙorafin nata a shafinta na X.
Idan ba’a manta ba gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun tsunduma yajin aiki a farkon mako daga ranar Litini inda su ka yi fatali da tayin naira dubu sittin a matsayin mafi ƙarancin albashi, sai dai sun dakatar da yajin aikin ne don ci gaba da tattaunawa da gwamnati amma kuma sai kwatsam ita ƙungiyar gwamnonin ta fito tana iƙirarin cewa hatta dubu sittin ɗin ma ba za ta iya biya ba.