Gwamnonin Kudu Maso Yamma Za Su Kafa Rundunar Tsaro Don Dakile Barazanar Tsaro

Gwamnonin yankin Kudu maso Yamma sun amince da kafa wata rundunar tsaro ta haɗin gwiwa domin shawo kan matsalolin tsaro a yankin.
A wata sanarwa da ƙungiyar gwamnonin yankin ta fitar bayan taron da ta gudanar a fadar gwamnatin Legas, ta bayyana cewa wannan mataki ya zama dole sakamakon rahotannin da ke nuna ɓullar ƴan ta’adda daga ƙungiyar ISWAP da sauran ƴan bindiga a yankin.
A farkon watan Janairu, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa ƴan bindiga da ake fatattakarsu daga wasu yankunan Arewacin Najeriya na kwararowa cikin wasu sassan jiharsa. Wannan lamari ya sa masu ruwa da tsaki, ciki har da ƙungiyar cigaban Yarabawa ta Afenifere, suka yi kira da a ɗauki matakin gaggawa don dakile barazanar.
Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne gwamnan Legas, ya ce rundunar za ta samu kayan aikin zamani, ciki har da jirage marasa matuƙa, don inganta aikinta.
Ƙungiyar gwamnonin yankin ta bayyana cewa yawaitar hare-haren ƴan bindiga barazana ce ga zaman lafiya da tsaron yankin baki ɗaya. Don haka, sabuwar rundunar za ta yi aiki tare da rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro.
Good info. Lucky me I reach on your website by accident, I bookmarked it.