March 28, 2025

Gwamnatin Yobe ta ƙaryata rade-radin amincewa da mafi ƙarancin albashin N70,000 ga ma’aikata

images (10) (18)

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnatin jihar Yobe ta yi watsi da wani sako da aka wallafa a dandalin sada zumunta na yanar gizo da cewa ta amince da naira 70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikatanta.

A cewar Darakta Janar na yaɗa labaran gwamnan jihar, Mamman Mohammed, “gwamnatin jihar Yobe ba ta fitar da wata sanarwa dangane da mafi karancin albashi ba.”

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar na ci gaba da aiki kan lamarin kuma za ta fitar da sanarwa kan sabon mafi karancin albashi da zarar ya kammala.

Mohammed ya bayyana wannan jita-jita a matsayin “rashin ta-ido, riga-kafi da kuma yaudara”.

Ya kuma lura cewa sakon ba shi da cikakkun bayanai kuma ya kasa bayyana lokacin da kuma inda bayanin ya fito, wanda ya sanya abubuwan da ke cikin “marasa kan gado.”

Ya shawarci jama’a da su “yi watsi da wannan magana ta yaudara” ya kuma ba da tabbacin cewa za a ba su wata sanarwa a hukumance mai inganci daga gwamnati.