February 10, 2025

Gwamnatin Tinubu na tsoron kama Yahaya Bello—Deji Adeyanju  

327
images (12) (10)

Daga Sabiu Abdullahi  

Lauyan kare hakkin bil’adama kuma mai fafutuka, Deji Adeyanju, ya zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaronta da tsoron cafke tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, bisa zargin karkatar da kudade naira biliyan 80.2 duk da umarnin kotu na kama shi.  

Adeyanju ya ce, “Ku je ku kama Yahaya Bello, me ya sa kuke tsoron Yahaya Bello? Bayan haka, Yahaya Bello ya raina kotu, kuma bai mutunta kotu ba, kotu ta bayar da umarnin a kama shi, amma gwamnati na tsoron kama Yahaya Bello.”  

Ya caccaki gwamnati kan yadda ta zaɓi murza gashin-baki a kan masu zanga-zangar lumana da ke zanga-zangar adawa da matsananciyar yunwa, wahalhalu da kuma rashin shugabanci nagari a Najeriya.  

Adeyanju ya bayyana cewa ‘yan kasar na da ‘yancin gudanar da zanga-zanga don haka kada su ji tsoro.  

A halin da ake ciki, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin wasu masu zanga-zanga 10 da aka kama bisa zarginsu da hannu a zanga-zangar #EndBadGovernance.  

327 thoughts on “Gwamnatin Tinubu na tsoron kama Yahaya Bello—Deji Adeyanju  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *