January 24, 2025

Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 50 Don Magance Matsalar Tsaro a Jihohi 5 na Arewa

4
IMG-20240112-WA0038.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Mataimakin shugaban kasa, Kahsim Shettima, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da shirin “Pulaaku Initiative”, wanda zai magance tashe-tashen hankula da ‘yan fashi da makami a Arewa, kuma ya ware naira biliyan 50 ga shirin, a karon farko.

“Pulaaku” dai kalmar Fulatanci ce da take nufin “jin kunya”.

A watan Yulin 2023 ne mataimakin shugaban kasar ya kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnatin jihar Kano kan rasuwar dattijon jihar, Abubakar Galadanci.

A lokacin ya bayyana cewa za a kaddamar da shirin na Pulaaku “nan da makonni biyu”, inda kuma ya nuna cewa yin amfani da sojoji kadai ba zai taimaka ba, wajen kawo ƙarshen rikicin yankin Arewa maso Yamma na kasar nan.

Da yake jawabi a lokacin bude taron kwana biyu kan rashin tsaro a Arewacin Najeriya, wanda kungiyar hadin kan Arewacin Najeriya ta shirya, mai taken “Hanyoyi da Yawa Na Magance Matsalar Tsaro a Arewacin Najeriya”, Shettima, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Ibrahim Hadeija, ya ce shirin da aka amince da shi a yanzu zai fara ne a jihohi biyar na Arewa wato Sokoto, Kebbi, Katsina, Benue, Zamfara, Neja da Kaduna.

A cewar, hakan zai gaggauto da arzikin yankin Arewa.

4 thoughts on “Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 50 Don Magance Matsalar Tsaro a Jihohi 5 na Arewa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *