Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Juma’a da Litinin Hutu Domin Babbar Sallah

Gwamnatin Najeriya ta bayyana ranakun Juma’a da Litinin, 6 da 9 ga watan Yuni 2025, a matsayin hutun bikin Babbar Sallah ga ma’aikatan gwamnati.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya, yana mai taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar wannan muhimmin biki na addini.
A ranar Juma’a, 6 ga Yuni ne Musulmi za su gudanar da sallar Idi tare da yanka dabbobin layya, wanda ke ɗaya daga cikin manyan ibadu a lokacin Babbar Sallah.
Gwamnatin ta bukaci Musulmi da su gudanar da bikin cikin zaman lafiya da kuma nuna ƙauna da tausayi ga juna, musamman ga marasa galihu.