May 17, 2025

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Daukar Ma’aikatan Da Janyewar USAID Ta Shafa

images-2025-02-17T163104.761.jpeg

Ministan Lafiya na Najeriya, Ali Pate, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na duba yiwuwar daukar ma’aikata 28,000 da ke aiki da Hukumar Agajin Amurka (USAID) a baya.

Da yake magana a wata hira da Channels TV ranar Juma’a, ministan ya ce wannan mataki na daga cikin shirin gwamnatin Najeriya na inganta ɓangaren kiwon lafiya, musamman bayan janye tallafin USAID.

Tun bayan hawansa mulki, Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci dakatar da tallafin samar da magunguna da ayyuka kamar kula da masu cutar HIV a ƙasashe masu tasowa, har sai an kammala bincike kan lamarin.

Ministan ya jaddada cewa Najeriya ba ta ware isassun kuɗaɗe ga ɓangaren lafiya ba, amma Shugaba Bola Tinubu na da niyyar sauya alƙiblar tsarin.

Haka nan, ya bayyana cewa fiye da kashi 70 na magungunan da ake amfani da su a Najeriya daga ƙasashen waje ake shigowa da su.