January 14, 2025

Gwamnatin Nijar za ta gyara alaƙa da Jamhuriyar Benin

0
IMG-20240606-WA0033.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnatin mulkin soji a Nijar ta yarda da tattaunawa da gwamnatin Jamhuriyar Benin karkashin jagorancin tsofaffin shugabannin kasar Benin guda biyu, domin taimakawa don dawo da dangantaka bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar a shekarar da ta gabata

Juyin mulkin dai ya kai ga rufe kan iyaka da kuma rufe wani bututun mai da China ke goya wa baya.

A cewar wani rahoto na TRTAfirka Hausa, amincewa da tattaunawar ta zo ne biyo bayan wata muhadasa da shugaban Nijar na soji Janar Abdourahamane Tiani da tsofaffin shugabannin kasar Benin Thomas Boni Yayi da Nicephore Soglo suka yi a ranar 24 ga watan Yuni.Sai dai hukumomin kasashen biyu sun faɗa wa Reuters a ranar Laraba cewa ba a riga an saka ranar da za a gudanar da taron ba.

Wani ƙuduri zai iya ba da damar sake dawo da tura man da ke kwarara zuwa kasar Sin ta bututun mai da PetroChina ke mara wa baya.

Nijar ta dakatar da fitar da mai ta bututun mai tsawon kilomita 2,000 zuwa gaɓar Tekun Benin a tsakar watan Yuni yayin da ake ta takun-saƙa game da rufe iyakokin.

Sai dai hukumomin kasashen biyu sun faɗa wa Reuters a ranar Laraba cewa ba a riga an saka ranar da za a gudanar da taron ba.

Wani ƙuduri zai iya ba da damar sake dawo da tura man da ke kwarara zuwa kasar Sin ta bututun mai da PetroChina ke mara wa baya.

Nijar ta dakatar da fitar da mai ta bututun mai tsawon kilomita 2,000 zuwa gaɓar Tekun Benin a tsakar watan Yuni yayin da ake ta takun-saƙa game da rufe iyakokin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *