January 14, 2025

Gwamnatin Neja za ta samar da asibitocin matakin farko guda 100 a faɗin jihar

0
images (10) (1)

Daga Sabiu Abdullahi     

Gwamnatin jihar Neja ta fara aikin gina rukunin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 100 a fadin kananan hukumomin jihar 25.     

Mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Abdullberqy Ebbo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Minna ranar Talata.     

A cewar Ebbo, aikin na daga cikin kokarin da gwamnati mai ci ke yi na tabbatar da “Sabuwar Ajandar Neja”.     

Ya bayyana cewa Gwamna Umar Bago ya sanar da cewa kusan 20 daga cikin cibiyoyin za su fara aiki nan take, yayin da wasu kuma za su yi koyi da su.     

Sai dai kuma wasu wurare biyu na Maitumbi FM da ke Bosso da Tsohuwar Gidan Marayu, Nasarawa C, a karamar Hukumar Chanchaga, ba su iya fara aikin ba saboda wasu ƴan matsaloli.     

Ebbo ya bayyana cewa aikin na da nufin samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya a tsakanin al’ummomi, tare da kawar da bukatar tafiye-tafiye mai nisa don neman magani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *