Gwamnatin Najeriya za ta ɓullo da sabon shiri mai kama da NYSC ga masu takardar NCE
Daga Sabiu Abdullahi
Ma’aikatar Ci Gaban Matasa ta Najeriya ta sanar da samar da wani sabon shirin horarwa irin na masu yi wa kasa hidima (NYSC) ga wadanda suka kammala karatun malunta a Najeriya, wato NCE.
Karamin Ministan Cigaban Matasa Mista Olawande Wisdom ne ya bayyana hakan a yayin bude sansanin BEMORE OYO 2024 a Ibadan ranar Litinin.
A cewar ministan, shirin na da nufin magance rashin horar da masu rike da takardar NCE.
An ambato shi yana cewa, “Babban abin da ma’aikatar ta sa a gaba shi ne ‘yan kasa da horar da su, kuma muna dawo da su, muna da NYSC ga wadanda suka kammala jami’a, amma wadanda suka gama NCE da sauran su fa?”
Ministan ya bayyana bukatar samar da shirin horarwa na jiha, inda ya ce, “Muna so mu samar da horo domin ba sai kun je wasu jihohi ku samu horarwar ba.
Ma’aikatar na shirin hada kai da ma’aikatar ilimi domin aiwatar da sauye-sauyen horarwa da suka hada da shirin da aka tsara na wadanda suka kammala NCE.
Ana sa ran wannan matakin zai samar da irin wannan dama ga masu rike da kwalin NCE don bunkasa kwarewarsu da bayar da gudummawarsu ga ci gaban kasa.