Gwamnatin Najeriya ta kira taron gaggawa da shugabannin ƙwadago saboda yajin aiki
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnatin Najeriya na gudanar da wani taro da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC kan yajin aikin da suke yi a fadin kasar, wanda ya kawo naƙasu a fannoni da yawa na ƙasar.
Jaridu sun rawaito cewa taron na gudana ne a ofishin mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribaɗu.
Waɗanda suka halarci taron sun hada da ministan kwadago Simon Bako Lalong, karamin minista Hon. Nkeiruka Onyeajeocha da shi kansa Nuhu Ribadu.
Haka kuma shugabannin kungiyar kwadago karkashin jagorancin shugaban kungiyar TUC, Festus Osifo, da babban sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja da sauran shugabannin kungiyar kwadagon duk sun halarta.
Idan ba a manta na, NLC da TUC sun tsunduma yajin aiki a duk fadin kasar, inda suka bukaci a kama wadanda ake zargin ‘yan daba da masu daukar nauyinsu, musamman waɗanda suka ci zarafin shugaban NLC.
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da aka kai wa shugaban NLC hari a Oweri, babban birnin jihar Imo a ranar 1 ga watan Nuwamba lokacin da ma’aikata a jihar suka gudanar da zanga-zanga kan rashin biyansu albashi.
скорая наркологическая помощь москва скорая наркологическая помощь москва .
наркология вывод из запоя ростов наркология вывод из запоя ростов .
листогибочный пресс листогибочный пресс .
Анонимное лечение игромании в Казахстане https://narcologiya-kazakhstan.kz .
масло моторное 5w40 таиф http://e-taif.ru .
instagram photo viewer http://www.anonstoriesview.com .