January 13, 2025

‘Gwamnatin Najeriya ta gaza cika alkawarin dakatar da karɓar harajin shigo da kayan masarufi’

0
Screenshot_2024-08-06-04-53-21-476_com.android.chrome~2

Daga Sabiu Abdullahi 

Duk da sanarwar da Shugaba Bola Tinubu ya bayar a watan Yuni na dakatar da harajin shigo da kayayyaki da kuma harajin kayan abinci na tsawon watanni shida, masu shigo da kayayyaki daga Najeriya sun yi ikirarin cewa har yanzu ana tilasta musu biyan wadannan kudade.    

Umurnin shugaban kasar da ke da nufin dakile tashin gwauron zabi na kayan abinci da kayan masarufi, ba a aiwatar da shi ba, a cewar kungiyar masu shigo da kaya ta Najeriya IMAN. 

“Kamar babu wani abu da ya canza, muna biyan haraji kamar yadda muka saba,” in ji Aminu Dan-Iya, Shugaban kungiyar IMAN a yankin Arewacin Najeriya.

“Jami’an kwastam suna gaya wa mambobinmu a wuraren shiga cewa ba su da wata sanarwa a rubuce game da dakatarwar.”   

Rashin aiwatar da wannan umurni ya haifar da tsaiko da biyan haraji, wanda ya saba wa manufar gwamnati na rage hauhawar farashin kayayyaki da daidaita farashin. 

Dan-Iya ya bayyana kwarin guiwar cewa tsarin dakatar da haraji na gajeren lokaci zai taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma haifar da raguwar farashin hatsi da kayan masarufi, wanda zai kawo sauki ga masu amfani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *