April 26, 2025

Gwamnatin Najeriya ta ƙara kudin yin fasfo

images (9) (4)

Daga Sabiu Abdullahi     

Gwamnatin tarayya ta amince da sake ƙara kudaden fasfo na Najeriya don tabbatar da ingancin takardar, daga ranar 1 ga Satumba, 2024.     

Sanarwar da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa ta fitar, ta ce littafin fasfo din mai shafuka 32 wanda yake da aiki na tsawon shekaru 5 a yanzu zai ci N50,000 daga N35,000.     

Littafin fasfo din mai shafuka 64 wanda yake aiki na tsawon shekaru 10 a yanzu zai ci N100,000 daga N70,000.     

Duk da haka, wannan canjin bai shafi ƴan Najeriya da suke ƙasashen waje na.     

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya ta yi nadamar duk wata matsala da ƙaruwar kuɗin ka iya haifarwa.

69 thoughts on “Gwamnatin Najeriya ta ƙara kudin yin fasfo

  1. продамус промокод скидка на подключение [url=http://krasnogorsk.anihub.me/viewtopic.php?id=18111#p23006]http://rubiz.forum.cool/viewtopic.php?id=3874#p139[/url] .

Comments are closed.