Gwamnatin Lagos ta rufe coci-coci da gidajen casu saboda hayaniya
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnatin jihar Legas ta yanke shawarar rufe coci-coci, mashaya, gidajen kwana, wuraren gudanar da bukukuwa da sauran cibiyoyi saboda hayaniyar muhalli.
Wuraren da wannan mataki ya shafa suna unguwanni ne kamar su Legas Island, Ojudu, Ogba, Magodo, da kuma Ikosi.
Jami’an Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Legas, LASEPA ne suka aiwatar da matakin na rufe wuraren.
Wannan na zuwa ne dai bayan koke-koken jama’a game da ƙararrakin lasifika da ke iya samunsu a lokutan da suke buƙatar hutu.





It is always great to come across a page where the admin take an actual effort to generate a really good article. Check out my website UY4 concerning about Thai-Massage.