Gwamnatin Kano za ta rushe katangar gidan Sarki da ke Nasarawa
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnatin jihar Kano za ta fara aikin rushe katangar gidan Sarki na Nasarawa da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ke ciki.
A cewar gwamnatin, za ta yi hakan ne “saboda ya lalace”.
Kwamashinan Shari’a na Kano Haruna Isa ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar a gidan gwamnati.
Gwamnatin ta kuma ba da umurni wa kwamishinan ‘yansandan jihar da ya fitar da Aminu Ado daga gidan bayan hukuncin kotu a yau Alhamis, wanda ta yi iƙirarin cewa ya ba ta nasara a kan ɓangaren da suka shigar da ƙarar.