Gwamnatin Kano za ta biya diyyar biliyan 3 ga ƴan kasuwar da aka rushe wa shaguna
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnatin jihar Kano ta zauna da masu shaguna da aka ruguza dukiyoyinsu bisa umarnin Gwamna Abba Yusuf, inda suka amince da biyan diyyar naira biliyan uku.
Rahotanni sun nuna cewa hakan ya zo ne a matsayin lallashi ga ‘yan kasuwar tare da kauce wa duk wani abu da ka iya gurgunta kudaden jihar.
A halin da ake ciki tun da farko sun bukaci naira biliyan 250, kuma sun sun yi nasara a kotu inda aka ba da hukuncin naira biliyan 30 a watan Satumba.
Sai dai jihar ta ki amincewa da hakan, lamarin da ya sa ‘yan kasuwar suka nemi a ba da umarnin a biya su daga asusun gwamnati.
A ranar Alhamis, lauyoyin bangarorin biyu sun sanar da mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja game da sasantawar da aka fara a ranar da ta gabata.
Ayagi, wanda ke wakiltar ‘yan kasuwar, ya bukaci kotun da ta shigar da karar a matsayin hukuncin amincewa, kuma lauyan jihar Matanmi bai yi watsi da hakan ba, yayin da mai shari’a Ekwo ya amince da bukatarsu.