January 14, 2025

Gwamnatin Kano ta fitar da maƙudan kuɗaɗe saboda wasu muhimman ayyuka

0
Abba-Yu.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da fitar da naira biliyan 40.353 domin gudanar da ayyuka daban-daban a jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Baba Halilu Dantiye, ya ce majalisar a taronta na 8, ta amince da naira biliyan 15.974 ga ma’aikatar ayyuka da gidaje don gina hanyar ƙarƙashin kasa ta Dan Agundi da gadar sama da naira biliyan 14.455 domin ginim gadar sama.

Dantiye ya ce, “Majalisar ta amince da fitar da naira biliyan 3.360 ga ma’aikatar ayyuka da gidaje domin sake duba farashin gina magudanan ruwa da aka rufe a bakin kogin Jakarta-Kwarin Gogau, yayin da aka samu naira biliyan don a yi hanyar Kofar Waika-Unguwar Dabai-Yan Kuje ta yamma a karamar hukumar Gwale.

“Hakazalika, an amince da kudi naira biliyan 1.350 ga ma’aikatar ayyuka da gidaje domin yin titin Unguwa Uku ‘Yan Awaki-Limawa Junction a karamar hukumar Tarauni.

Daga cikin kuɗaɗen da aka miƙa wa ma’aikatar ayyuka da gidaje domin gudanar da ayyuka daban-daban sun haɗa da naira miliyan 802.695 domin kammalawa da kuma aikin titin Kofar Dawanau-Dandinshe-Kwanar Madugu Road Phase ll.

An sake ware naira miliyan 458.443 domin sake bayar da kwangilar gina gadar masu tafiya a ƙafa na kankare a wurare daban-daban a faɗin jihar, yayin da aka amince da naira miliyan 420 don gyara fitilun manyan tituna.

Majalisar ta kuma amince da bayar da Naira miliyan 200.537 ga ma’aikatar ayyuka da gidaje domin biyan wasu makudan kudade dangane da kwangilar gyaran hanyar Kwanar Kwankwaso da ke karamar hukumar Madobi da kuma Naira miliyan 107.658 na gyaran hanyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *