June 14, 2025

Gwamnatin Kano na shirin tilasta wa kamfanoni daukar kashi 75 na ma’aikata ’yan asalin jihar

IMG-20250331-WA0006

Gwamnatin Jihar Kano na shirin kafa wata doka da za ta tilasta wa kamfanonin da ke aiki a jihar su rika daukar akalla kashi 75 cikin 100 na ma’aikatansu daga cikin ’yan asalin Kano.

A wani mataki na ganin an aiwatar da wannan kuduri yadda ya kamata, gwamnatin ta kafa kwamitin da zai sa ido kan yadda ake daukar ma’aikata a hukumance.

Da yake jawabi yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a jiya Laraba a Kano, shugaban kwamitin, Dakta Ibrahim Garba, ya ce za a mika daftarin dokar ga majalisar dokoki ta jihar da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf domin amincewa.

Ya bayyana cewa wannan doka na da nufin rage matsalar rashin aikin yi da kuma zaman banza da ke addabar matasa a jihar.

Dakta Garba ya kara da cewa Gwamna Abba ne da kansa ya kafa kwamitin sakamakon korafe-korafen da al’ummar Kano ke yi dangane da yadda wasu kamfanoni ke kin daukar ’yan asalin jihar aiki, duk da cewa suna cin moriyar tattalin arzikin jihar.