Gwamnatin Jihar Taraba ta raba ₦524m ga mutane 10,409
Daga Abdullahi I. Adam
Mataimakin gwamnan jihar Taraba, Aminu Alkali, ya sanar da cewa jihar na ƙara faɗaɗa hanyoyin agaza wa mutane domin ganin tallafin da jihar ke badawa ya isa ga masu ƙaramin ƙarfi a faɗin jihar.
Aminu Alkalin ya kuma yi nuni da cewa gwamnatin jihar na da matuƙar sha’awar ganin ta rage wa marasa galihu wahalhalun da suke fuskanta ta hanyar bayar da tallafi ga mabuƙata.
Mataimakin gwamnan ya bayyana hakan ne a ƙarshen mako a Jalingo, babban birnin jihar, a lokacin da ake rabawa mutane 10,409 naira miliyan 524.
Haka zalika, Alkalin ya bayyana ƙwarin guiwar cewa idan aka yi la’akari da yadda gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen yaƙar talauci, nan ba da daɗewa ba Taraba za ta fice daga jerin jahohi da ke da marasa galihu.
Kamar yadda mataimakin gwamnan ya ce, “Kashi na farko da na biyu na waɗanda suka ci gajiyar wannan tallafin sun kasance matasa da mata 2,680 ne.
“Wannan kashi na uku ya shafi masu cin gajiyar tallafin ne su 10,449 a fadin ƙananan hukumomin jihar 16 da kuma yankunan cigaba na musamman guda 2.
“Muna tallafa musu don faɗaɗa ƙanana da matsakaitan sana’o’insu da kuma tabbatar da farfaɗo da tattalin arziƙin cikin gida domin samar da ƙarin ayyukan yi.
“Da abin da muke yi, muna fatan cewa a cikin shekara guda mai zuwa, Taraba ba za ta sami tarihin marasa galihu ba.”
Ya kuma buƙaci waɗanda suka amfana da su yi amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata.
Kwamishinan ƙungiyoyin taimakon kai-da-kai da yaƙi da fatara na jihar, James Habu, wanda shi ma ya yi magana a wajen rabon tallafin, ya ce an bai wa waɗanda suka ci gajiyar tallafin naira 50,000 kowannensu a matsayin tallafi.
Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa a kashi na farko an raba naira miliyan 101.9 ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin, yayin da aka raba naira miliyan 100 a kashi na biyu.
A cewarsa, “Gwamnatin jihar ta ƙara adadin waɗanda suka ci gajiyar tallafin a kashi na uku zuwa sama da 10,000, wanda hakan ya sa aka raba naira miliyan 524.
“Gwamnatin nan tana son kawar da talauci, kuma mun himmatu don cimma wannan manufa.”