Gwamnatin jihar Ribas ta ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa 85,000
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnatin jihar Rivers ta sanar da amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi na naira 85,000 ga ma’aikatan jihar.
Shugaban ma’aikatan jihar, George Nwaeke, ya bayyana cewa gwamnan jihar, Sim Fubara, ya amince da sabon albashin ne yayin wani taro da aka gudanar tsakanin wakilan gwamnati da ƙungiyar ƙwadago ta jihar, kamar yadda Channels ta ruwaito.
Nwaeke ya ce fara aiki da wannan sabon albashi zai yiwu nan take ba tare da wani jinkiri ba.
A nashi bangaren, shugaban kwamitin tattaunawa, Chukwu Emecheta, ya yabawa gwamna Fubara bisa amincewa da bukatar ma’aikatan.
Haka zalika, shugaban ƙungiyar kwadago ta jihar, Alex Agwanwor, ya bayyana cewa sabon mafi ƙarancin albashin zai taimaka wajen rage wa ma’aikatan jihar radadin tsadar rayuwa da ake fuskanta.