January 15, 2025

Gwamnatin jihar Abia ta musanta karɓar tallafin shinkafa daga gwamnatin tarayya

0
images-6-16.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi      

Gwamnatin jihar Abia ta karyata ikirarin cewa ta karbi tirela 20 na shinkafa a matsayin tallafi daga gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu.     

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Prince Okey Kanu ya bayyana cewa, “Ba mu ga wata motar shinkafa daga Gwamnatin Tarayya ba, kuma batun sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 kan Naira 40,000 labari ne na karya.     

Kanu ya sake nanata cewa gwamnatin jihar ba ta amfani da jita-jita, kuma babu wata sanarwa da aka samu daga gwamnatin tarayya dangane da abin da ya shafi tallafi.     

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta sanar da raba tireloli 20 na shinkafa ga kowace jiha domin rage radadin tsadar kayan abinci.     

Baya ga wannan, Edo da Adamawa su ma sun musanta karbar wannan shinkafar, lamarin da ya janyo cece-kuce.     

Ministan Neja-Delta ya mayar da martani cewa gwamnonin jihohi na rashin adalci ga shugaba Tinubu, wanda hakan ke nuna cewa wasu gwamnonin ne suka tsara lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *