Gwamnatin Borno Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Nazarci Rikicin Manoma Da Makiyaya
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnatin jihar Borno ta kafa kwamitin mutum 10 da zai binciki musabbabin rikici tsakanin manoma da makiyaya a fadin jihar da nufin magance su.
Kwamitin dai zai “sake kafa dusassun hanyoyin kiwon shanu da kuma gano wuraren kiwo da ba a yin amfani da su sosai ba.”
Gwamna Babagana Zulum ya kaddamar da dokokin kwamitin a garin Gamboru da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru a ranar Litinin.
Ya ce dokokin kwamitin na daya daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke dauka domin dakile rikicin manoma da makiyaya a fadin jihar.