February 10, 2025

Gwamnatin Birtaniya ta hana wasu ɗalibai daga Najeriya tafiya karatu da iyalansu

94
images-2024-01-02T055333.788.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Ma’aikatar cikin gida ta Birtaniya a ranar Litinin ta sanar da fara aiwatar da manufofinta na hana daliban Najeriya da sauran daliban kasashen ketare shigo da wadanda suka dogara da su ta hanyar biza karatu.

A cikin wani rubutu a kan X (watau Twitter), Ofishin Cikin Gida ya sake nanata cewa kawai waɗanda ke kan binciken digiri na biyu ko ɗaliban tallafin karatu na gwamnati ne kawai za a keɓe su daga wannan sabuwar dokar.

“Mun himmatu sosai don ganin an rage ƙaura. Daga yau, sabbin ɗalibai na ƙasashen waje ba za su ƙara iya kawo danginsu zuwa Birtaniya ba. Amma masu binciken karatun digiri na biyu ko kuma ɗaliban tallafin karatu na gwamnati banda su a ciki, ”in ji Ofishin Cikin Gida.

An ba da rahoton cewa a watan Mayun 2023, Burtaniya ta kafa wata doka ta hana daliban Najeriya, da sauran masu karatu a Burtaniya kawo iyali a matsayin masu dogaro da su sai dai a wasu yanayi.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar Birtaniya ke da niyyar dakile bakin haure cikin kasar wanda ya kai kusan miliyan daya.

A karkashin sabuwar dokar, Birtaniya za ta cire izinin barin daliban kasashen waje su bar amfani da bizarsu ta dalibai don komawa zuwa ga bizar aiki kafin su kammala karatunsu.

94 thoughts on “Gwamnatin Birtaniya ta hana wasu ɗalibai daga Najeriya tafiya karatu da iyalansu

  1. Attractive sewction of content. I just stumbled upoin your wevlog and
    iin acdcession capital to assert that I acqwuire in fact enjoyed accoujt your blog posts.
    Any waay I’ll be subscribing too your fdeds and even I achieveent yoou accesss
    consistently rapidly.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *