Gwamnatin Bauchi ta ba da tallafi ga al’ummar da suka rasa matsagunansu A Toro
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnatin jihar Bauchi ta ɗauki matakai na tallafa wa al’ummomin da suka rasa matsagunansu a Mangun Jihar Filato.
Sama da ‘yan gudun hijira 2,085 a kauyuka biyar nenda suka kwararo karamar hukumar Toro suka sami tallafin kayan abinci da kudi a wani shirin raba kayan agaji.
‘Yan gudun hijirar da suka nemi mafaka a kauyukan Tilden Fulani, Gwaljarandi, Magama Kara, Gajaule, da Takanda sun samu tallafin kayayyakin masarufi da suka hada da buhunan masara 100, buhunan shinkafa 65, galan-galan ɗin mai 25, maggi 5, 5, buhunan gishiri, katifu 135, barguna 135, kayan abinci iri-iri, da tsabar kudi naira miliyan daya.
Taron rabon kayayyakin ya samu jagorancin kwamishiniyar Agaji ta Jiha Hon Hajara Yakubu Wanka.
A jawabinta ga ‘yan gudun hijirar, kwamishiniyar ta nuna alhinin gwamnan tare da bayyana kudirin gwamnatina tantance bukatunsu.
Idan mai karatu bai manta ba, a ƴan sakonnin da suka gabata, an samu rikice-rikice a Mangun Jihar Filato wanda ya raba mutane dubbai da muhallansu.