Gwamnatin Najeriya za ta taƙaita shagulgulan bikin ƴancin kai saboda ‘matsin rayuwa’
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar takaita shagulgulan bikin samun ‘yancin kan Najeriya da zai gudana a ranar 1 ga watan Oktoba mai kamawa saboda halin matsin da ake ciki a kasar.
A hirarsa da manema labarai yayin baje kolin shagulgulan da aka tsara gudanarwa a ranar bikin samun ‘yancin kan, sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya ce gwamnatin Najeriya tana sane da ‘yan Najeriya game da halin matsin tattalin arzikin da suke ciki.
Saboda haka, a cewarsa, aka takaita shagulgulan da za a gudanar a bikin.
An takaita shagulgula a bikin samun ‘yancin kan Najeriya na 63 a bara inda Sanata Akume, yace ba za a gayyaci shugabannin kasashen ketare ba, saboda halin matsi da ake ciki.
Akume, a wata ganawa da ya yi ranar Alhamis, ya ce an yanke shawarar ne a bisa la’akari da halin da kasa ke ciki, don haka Shugaba Tinubu ya amince a takaita shagulgula a bikin ‘yancin kan Najeriya na 64.