April 18, 2025

Gwamnan Katsina Ya Yi Rashin Mahaifiyarsa

FB_IMG_1742727872914

Mahaifiyar Gwamnan Katsina, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, ta rasu tana da shekaru 93.

Fadar gwamnatin jihar ta Katsina ce ta sanar da rasuwarta a yau Lahadi, amma ba ta bayyana musabbabin mutuwarta ba.

Sanarwar da Ibrahim Kaula Mohammed, babban sakataren yaɗa labarai na gwamna, ya fitar ta ce za a yi jana’izarta da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a yau.

Daga cikin ‘ya’yan da ta bari har da mai garin Radda, Kabir Umar Radda, da kuma Hauwa Umar Radda, tsohuwar matar marigayi tsohon shugaban Najeriya, Umar Musa Yar’adua.

Za a yi jana’izar a garin Radda, kimanin kilomita 70 daga Katsina, babban birnin jihar.