Gwamnan Katsina Ya Bukaci Jama’a Da Su Kare Kansu Daga Harin Ƴan Bindiga
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya yi kira ga jama’a da su ɗauki matakin kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.
A yayin wani taron gaggawa na tsaro da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Katsina a ranar Juma’a, Gwamna Radda ya jaddada muhimmancin kiyaye al’umma da kuma kare kai.
Taron wanda ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da sarakunan Katsina da Daura, Dr. Abdulmumini Kabir Usman da Dr. Umar Farouq Umar, ‘yan kasuwa, da shugabannin tsaro, an gudanar da shi ne domin tunkarar kalubalen tsaro da ke addabar jihar.
Gwamna Radda ya jaddada bukatar al’ummomi su hada kansu tare da kafa kungiyoyin kare kai daga hare-haren ‘yan bindiga, maimakon dogaro da tsoma bakin gwamnati kawai.
Ya tabbatar da aniyar gwamnati na tallafa wa irin wadannan ayyuka na al’umma ta hanyar horaswa da taimakon kayan aiki.
Da yake karin haske game da wasu damuwoyin da suka wuce rashin tsaro, Gwamna Radda ya yi magana game da hauhawar farashin abinci da kuma barazanar yunwa a tsakanin jama’a.
Ya amince da zanga-zangar da aka yi a fadin kasar sakamakon tashin gwauron zabin kayan masarufi, ya kuma jaddada wajabcin daukar matakan da suka dace don dakile al’amura a jihar Katsina.