Gwamnan Kano Abba Kabir ya tafi Kotun Ƙoli bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf wanda kotun daukaka kara ta tabbatar da tsige shi, ya bayyana aniyarsa na kalubalantar hukuncin a kotun koli.
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun, inda ta kori Yusuf tare da bayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.
A wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin a daren Juma’a, Gwamna Yusuf ya tabbatar da aniyarsa ta maido da abin da ya ke ganin hakkinsa ne.