November 5, 2024

Gwamnan jihar Kano ya ba da umarnin rufe asusun ajiyar bankin ma’aikatun jihar

0

Daga Sabiu Abdullahi  

Gwamna Kabiru Abba Yusuf na jihar Kano ya bayar da umarni ga Akanta-Janar na jihar da ya rufe asusun ajiyar banki na ma’aikatu da hukumomi ba tare da ɓata lokaci ba.  

Gwamnan ya ba da umarnin ne a ci gaba da zama da shugaban hukumar tara haraji ta jihar Kano da shugabannin MDA a gidan gwamnati.

Ya bayyana cewa an yanke wannan shawarar ne domin ganin an yi lissafin duk wani abu da gwamnati ta samu da kuma amfani da shi wajen ci gaban jihar.  

A cewar gwamnan, an dauki matakin ne da nufin tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin tafiyar da kudaden gwamnati.  

Ana sa ran rufe asusun bankunan zai daidaita harkokin hada-hadar kudi da kuma rage almundahana da kudaden jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *