January 15, 2025

Gwamna Zulum Ya Jaddada Aniyarsa ta Ci Gaba Da Ƙulla Alaƙa Da Ƙasar Chadi

1
IMG-20241107-WA0010.jpg

Daga Adamu Aliyu Ngulde

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya jaddada kuɗurinsa na karfafa dangantakar tattalin arziki da ƙasar Chadi, domin farfado da harkokin kasuwanci da zamantakewar al’umma.

Wannan ya biyo bayan koma bayan da rikicin Boko Haram ya haifar a tsawon shekaru a kasashen yankin sahel.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Chadi karkashin jagorancin Janar Abdulkarim Idris Derby Itno, wadanda suka kai ziyara domin nuna alhini game da bala’in ambaliyar ruwa da ya afku a birnin Maiduguri ranar 10 ga watan Satumbar wannan shekarar.

1 thought on “Gwamna Zulum Ya Jaddada Aniyarsa ta Ci Gaba Da Ƙulla Alaƙa Da Ƙasar Chadi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *