January 15, 2025

Gwamna Namadi ya halarci jana’izar sama da mutane 100 da wutar tanka ta hallaka a Majia
 

4
IMG-20241016-WA0006.jpg

Daga Sabiu Abdullahi
 
Gwamna Namadi na Jihar Jigawa ya halarci jana’izar sama da mutane 100 da suka rasa rayukansu sakamakon wata gobarar tankar mai da ta auku a garin Majiya, ƙaramar hukumar Taura, a daren Litinin.
 
Wannan mummunan ibtila’in ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwan mutane, yayin da wasu da dama ke karɓar magani a asibitoci daban-daban.
 
A jawabinsa, Gwamna Namadi ya nuna alhini ga al’ummar Majiya tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan al’amari.
 
Ya tabbatar wa al’ummar da abin ya shafa cewa gwamnatin jihar Jigawa za ta taimaka musu domin rage radadin wannan musiba.
 
Haka zalika, gwamnan ya bayyana cewa gwamnati za ta ɗauki nauyin maganin waɗanda ke jinya a asibitocin Hadejia, Ringim, Gumel, Jahun, da Dutse.
 
Bugu da ƙari, ya bayar da umarnin kai waɗanda suka ji munanan raunuka zuwa asibitin koyarwa na Aminu Kano da asibitocin gwamnatin tarayya na Nguru da Birnin Kudu domin samun kulawa ta musamman.

4 thoughts on “Gwamna Namadi ya halarci jana’izar sama da mutane 100 da wutar tanka ta hallaka a Majia
 

  1. Wondeerful site you have here butt I was wondering if yyou knew off aany user discussion forums that cover thhe sae topics taoked abiut iin tjis article?
    I’d really ike too be a part off onlibe community wuere I
    can gett opinions from other experienced people thaat share thhe sam interest.

    If you hzve anyy recommendations, please let me know.
    Cheers!

  2. We’re a ggroup of volunteers aand starting a new scheme
    inn our community. Yoour ite providded uus
    with valuable informaion tto work on. You’ve done a formidable joob andd ourr entiore community will bbe thankful to you.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *