June 14, 2025

Gwamna Fubara Ya Tabbatar Da Bin Hukuncin Kotun Koli Kan Zaɓen Kananan Hukumomi

download.jpeg

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa za ta bi hukuncin kotun koli bayan nazarin cikakken bayani da ke cikin hukuncin.

Yayin wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar a ranar Lahadi, Fubara ya ce gwamnatinsa za ta ba wa hukumar zaɓen jihar haɗin kai domin shirya sabon zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi, bayan kotun koli ta soke wanda aka gudanar a shekarar da ta gabata.

A ranar Juma’a, kotun koli ta rushe zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar da aka gudanar a ranar 5 ga Oktoba, 2024.

Gwamnan ya umarci shugabannin ƙananan hukumomin da aka soke zaɓensu da su miƙa ragamar mulki ga daraktocin mulki na ƙananan hukumomi daga ranar Litinin, 3 ga wata.

Haka nan, ya bayyana shirin naɗa shugabannin riƙo har sai an gudanar da sabon zaɓe.

1 thought on “Gwamna Fubara Ya Tabbatar Da Bin Hukuncin Kotun Koli Kan Zaɓen Kananan Hukumomi

Comments are closed.