Gwamna Diri ya sake lashe zaɓen gwamna a Bayelsa
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnan jihar Bayelsa mai ci Douye Diri ya sake yin nasara a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.
Sanarwar nasarar ta fito ne a hukumance daga bakin Farfesa Faruq Kuta, jami’in kula da masu kada kuri’a kuma mataimakin shugaban jami’ar Fasaha ta tarayya da ke Minna, a wurin tattara sakamakon zaben a ranar Litinin.
Gwamna Douye Diri ya samu nasarar lashe zaben ne da kuri’u 175,196, inda ya zarce babban abokin takararsa, Timipre Sylva na jam’iyyar All Progressives Congress, wanda ya samu kuri’u 110,108.
Jam’iyyar Labour ta samu kuri’u 905 a zaben.