December 7, 2025

Gwamna Abba Ya Nemi Gwamnan Edo Ya Biya Diyyar Mafarauta Da Aka Kashe

IMG-20250331-WA0006

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, da ya tabbatar da biyan diyyar mafarauta da aka kashe a jiharsa ta Edo yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida domin bukuwan Sallah.

Gwamnan Kano ya yi wannan roƙo ne lokacin da Gwamna Okpebholo ya jagoranci tawagar gwamnatinsa zuwa Kano domin jajantawa gwamnatin Kano da al’ummar jihar bisa harin da ya yi sanadin mutuwar matafiya a makon jiya.

A cikin jawabinsa, Gwamna Abba ya yaba da matakan da Gwamna Okpebholo ya ɗauka kan lamarin, inda ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta ɗauki matakan da suka dace domin hana ramuwar gayya, “domin mutanen Kano masu son zaman lafiya ne da maraba da baƙi.”

“Yawancin waɗanda aka kashe ɗin ƴan Kano ne. An tare su ne a jiharka a hanyarsu ta dawowa daga Fatakwal, aka gana musu azaba, sannan aka ƙone wasu daga cikinsu,” in ji Gwamna Abba.

Gwamnan ya kuma jinjinawa gwamnatin Edo kan yadda ta tabbatar da ɗauko gawarwakin tare da binne su kamar yadda addini ya tanada, da kuma kama waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.

Sai dai Gwamna Abba ya bayyana cewa yana da buƙatu biyu da yake so a cika domin tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa.