February 10, 2025

Gobarar Dajin Amurka Ta Lalata Gidaje Dubu 12 A Los Angeles

1
images-2025-01-11T172436.731.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Gobarar dajin da ta tashi a yankin Los Angeles ta lalata gine-gine kimanin dubu goma sha biyu tare da tilasta wa mutane sama da dubu ɗari da arba’in barin gidajensu.

A halin yanzu, jami’an kashe gobara na ci gaba da ƙoƙarin shawo kan wutar, amma masu hasashe sun gargadi cewa dawowar iska mai ƙarfi a ranakun Asabar da Lahadi na iya ƙara rura gobarar, musamman ma a yankin da ba a samu ruwan sama ba tun tsawon watanni takwas.

Rahotanni sun nuna cewa, aƙalla mutane goma sha ɗaya sun rasa rayukansu tun bayan tashin gobarar a ranar Talata.

A wani labari na daban, hukumar kashe gobara ta Los Angeles ta musanta rahotannin da ke cewa an kori shugabanta, Kristin Crowley, bayan da ta soki magajin garin birnin kan ƙarancin ma’aikata da kayan aiki a sashen kashe gobara.

Gbarar ta bar mazauna Los Angeles cikin damuwa yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ayyukan ceto da shawo kanta.

1 thought on “Gobarar Dajin Amurka Ta Lalata Gidaje Dubu 12 A Los Angeles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *