January 14, 2025

Gobara ta laƙume dukiya mai tarin yawa a Kantin-Kwari da ke Kano

2
images (14) (3)

Daga Sabiu Abdullahi  

Wata mummunar gobara da ta kama a babbar kasuwar Kantin-Kwari ta Kano a daren ranar Asabar ta lalata kayayyaki da kadarori na miliyoyin naira.  

Rahotanni sun nuna cewa masu shagunan sun fafata sosai domin ganin sun shawo kan gobarar, amma kokarinsu ya ci tura.  

Alhaji Hamisu Sabo wanda dan kasuwa ne a kasuwar, ya bayyana wa jaridar Blueprint a Najeriya abin da ya faru da shi.  

A cewarsa, wani ne ya kira shi da misalin karfe 7:30 na yammacin Asabar cewar kasuwa fa tana ta ci da wuta.

Da isarsa wurin shaguna biyu ne kawai suka kone, amma daga baya komai sai ya canja—wuta sai ƙaruwa take yi. 

Kasuwar Kantin-Kwari ta kasance babbar cibiyar kasuwancin saƙa da tufafi a Najeriya da yankin Sahara na Afirky, lamarin da ya sa gobarar za ta zama babbar illa ga tattalin arzikin yankin.  

A halin yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, inda hukumomi ke kokarin gano musabbabin tashin gobarar.

2 thoughts on “Gobara ta laƙume dukiya mai tarin yawa a Kantin-Kwari da ke Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *