November 8, 2025

Gobara ta hallaka dabbobi 78 a ƙauyen Danzago na jihar Kano

images-2025-02-07T065402.830.jpeg

Wata gobara da ta tashi a ƙauyen Danzago da ke ƙaramar hukumar Dambatta ta janyo asarar shanu biyu, tumaki 36, akuyoyi 17 da kuma kaji 10.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce lamarin ya faru ne a wani gida da aka fi sani da Gidan Ado Yubai ranar Laraba.

Ya bayyana cewa gobarar ta ƙone ɗakuna kusan 17 da rumbunan ajiya 19. Hukumar kashe gobara ta samu nasarar ceto wasu dabbobi da kuma kayayyakin ajiya.

Ya kara da cewa ba a samu asarar rai ba, amma wani jami’insu ya samu ƙuna a kafarsa yayin da yake kokarin kashe wutar.

2 thoughts on “Gobara ta hallaka dabbobi 78 a ƙauyen Danzago na jihar Kano

Comments are closed.