November 8, 2025

Gobara ta ƙone shaguna fiye da 300 a kasuwar wayoyi ta Kano

images (36)

Daga Sabiu Abdullahi

Wata gobara mai ƙarfi da ta tashi a kasuwar sayar da wayoyi da kayan gyara da ke cikin birnin Kano ta yi sanadin asarar dukiya da shaguna masu tarin yawa.

Shugaban kasuwar, Ambasada Jamilu Bala Gama, ya shaida wa manema labarai cewa gobarar ta ci gaba da tashi har na tsawon sa’o’i shida zuwa bakwai, tana ƙone kaya babu ƙaƙƙautawa.

Ya bayyana cewa fiye da shaguna 300 ne gobarar ta shafa, inda mafi yawan su ke ɓangaren da ake sayar da wayoyi da kayan gyaransu.

A cewarsa, “a wasu shagunan, akwai kaya da darajarsu ta kai naira miliyan 500, wasu har biliyan guda – amma duka sun ƙone kurmus.”

Ambasada Jamilu ya ƙiyasta adadin asarar da aka yi a gobarar da cewa ya kusa kai naira biliyan 100, yana mai cewa hakan babban koma baya ne ga ƴan kasuwar da lamarin ya rutsa da su.

Ya kuma bayyana cewa zuwa yanzu, ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba, amma hukumomi na ci gaba da bincike.

A Najeriya dai, irin waɗannan gobara a kasuwanni ba sabon abu ba ne, kuma masana na danganta su da rashin bin ƙa’ida da tsari wajen gine-gine da amfani da wutar lantarki a irin waɗannan wurare.