Galatasaray Za Su Kai Ƙarar José Mourinho Kan Zargin Nuna Wariyar Launin Fata

Kungiyar Galatasaray ta bayyana shirinta na kai rahoton kocin Fenerbahçe, José Mourinho, gaban hukumar UEFA da kuma hukumar kwallon kafa ta Turkiyya kan zargin nuna wariyar launin fata.
Wannan na zuwa ne bayan da Mourinho ya furta cewa, “[Ƴan wasan] benci na Galatasaray na tsalle-tsalle kamar birrai,” yayin da kungiyoyin biyu suka tashi 0-0 a wasan da suka kara jiya.
Hukumar Galatasaray ta ce ba za ta amince da irin wannan furuci ba, kuma tana bukatar hukunci mai tsauri kan Mourinho.
A halin yanzu, Galatasaray na kan gaba a teburin gasar Super Lig da tazarar maki shida tsakaninsu da Fenerbahçe, yayin da ake da sauran wasanni 14 a kakar bana.