G-Fresh zai gurfana gaban kotu, inji Hisba

Daga Abdullahi I. Adam
Jami’an hukumar Hisbar a jihar Kano sun kama Al’ameen G-Fresh, kuma kamar yadda babban daraktan hukumar, Mallam Abba Sufi ya shaida wa BBC Hausa, hukumar ta kama G-Fresh ɗin ne saboda laifuka masu alaƙa da yaɗa baɗala a shafukansa na sada zumunta.
Malam Abba Sufi ya ce sun kama matsahin ne bayan sun sha jan hankalinsa da ya daina wallafa abubuwa da suka keta shari’a a shafukan nasa amma ya ƙi.
”Mun kama shi ne bayan tarin gargaɗi da nasiha da muka sha yi masa kan abubuwa na baɗala da rashin kunya da yake wallafawa a shafukansa na sada zumunta,” inji Sufi.
Al’ameen G-Fresh zai gurfana gaban kotu a yau Litini inji hukumar ta Hisba domin fuskantar hukunci.
Shi dai G-Fresh fitacce ne wajen amfani da kafafen sada zumunta duk da an fi saninsa a TikTok, kuma abubuwan da ya ke yaɗawa a shafukan sun kauce ma tarbiyya kamar yadda hukumar ta Hisba ke iƙirari.
Ida ba mu manta ba, ko a watannin baya sai da hukumar Hisbar ta Kano ta kama wata matshiya mai suna Murja Kunya kan zargin amfani da kafafen sada zumuntan ba bisa ƙa’ida ba, kuma a yanzu haka lamarin Murjan na gaban kotu don jiran yanke hukunci.