November 8, 2025

Fursunoni 12 A Kogi Sun Tsere Daga Gidan Yari

images - 2025-03-24T131751.709

Aƙalla fursunoni 12 ne suka tsere daga gidan gyaran hali na gwamnatin tarayya da ke Kotonkarfe, Jihar Kogi, a safiyar ranar Litinin.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa an riga an kama ɗaya daga cikin waɗanda suka tsere.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa tana aiki tare da jami’an tsaro domin gano yadda fursunonin suka samu damar tserewa, tare da ɗaukar matakan hana maimaituwar irin haka.

Fanwo ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa, “Yadda fursunonin suka iya tserewa ba tare da barin wata alama ba abin mamaki ne. Dole ne a gudanar da bincike mai zurfi, a kamo duk wanda ya tsere, tare da gano duk wani da ke da hannu a lamarin.”