December 7, 2025

Fitaccen Malamin Addinin Islama, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, Ya Rasu

FB_IMG_1743736708939

An tabbatar da rasuwar sanannen malamin addinin Islama, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, a ranar Juma’a, 4 ga Afrilu, 2025, bayan fama da jinya.

Mutuwarsa ta girgiza al’ummar Musulmi, inda malaman addini da mabiyansa ke bayyana alhinin su.

Dr. Abdulaziz ya shahara wajen yada ilimin addini, tare da fafutuka a harkokin kasuwanci da noma.

A shekarun baya, ya fuskanci matsaloli na shari’a, inda aka bayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin tunzura jama’a.

Sai dai daga bisani, bayan wani sulhu da gwamnatin Bauchi ya koma gida.

Mutuwarsa ta bar babban gibi a fagen ilimi da wa’azi, inda ake jiran sanarwa game da shirye-shiryen jana’izarsa.