First Bank ya musanta shirin yin gyaran da zai hana kwastomomi mu’amala da manhajojinsa
Daga Sabiu Abdullahi
First Bank ba Najeriya ya karyata rahotannin da ke cewa za a sabunta tsarin bankin kuma ya ba da tabbacin cewa kwastomomi ba za a samu cikas ba ga ayyukansu.
Bankin ya bayyana cewa tsarin sabuwar manhaja da ke amfani da tsarin girgije (watau cloud a Turance), yana da alaka ne kawai ga masu samar da kaya ba ga kwastomomi ba.
A wata sanarwa, shugabannin bankin sun yi kira ga kwastomomi da su yi watsi da rahotannin da ba su da tushe kuma su nemi sahihiyar magana daga kafafen bankin. “Muna son mu yi bayani game da rahoton da ake yadawa cewa za a sabunta tsarin aiki a FirstBank.”
Sanarwar ta ce, “Babu wani tsarin sabuntawa a halin yanzu, kuma duk wasu manhajojinmu na kwastomomi suna aiki yadda ya kamata. Ba mu da wata matsala ga ayyukanmu.”
Bankin ya sake tabbatar da jajircewarsa wajen ba da ingantaccen aiki ba tare da tsaiko ba, domin kwastomomi su ci gaba da samun ayyukan banki cikin kwanciyar hankali.
Parks and rec cast. 777. Ny rangers. Dr strangelove. Frank sinatra.
Close.