January 14, 2025

Filato: Majalisa ta gayyaci jagororin hukumomin tsaro saboda munanan hare-harem da aka kai

37
Senate.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

A yau Asabar ne majalisar dattawa ta gayyaci shugabannin hukumomin tsaro kan kisan gillar da aka yi wa mutane sama da 100 a jajibirin Kirsimeti a jihar Filato.

Akalla mutane 145 ne aka kashe a harin da ‘yan bindiga suka kai kauyuka 23 a kananan hukumomin Bokkos da Barikin Ladi na jihar Filato.

Hare-haren, wadanda kuma suka yi sanadin jikkata daruruwan mutane tare da lalata dukiyoyi, an ce an kai su ne tun daga daren ranar Asabar zuwa safiyar Litinin.

Majalisar dattijai ta ce saboda hada kai da ‘yan bindigar suka yi kisan gilla, hakan ya nuna cewa an gaza samun bayanan sirri na tsaro.

Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi), wanda ke jagorantar kungiyar Sanatocin Arewa, ya bayyana harin a matsayin wanda ba a taba gani ba.

Dan majalisar ya ce sakamakon binciken da ya yi bayan shafe sa’o’i 72 a Filato tare da ganawa da gwamnan jihar, ya nuna cewa maharan tare da hadin gwiwar mazauna yankin sun kai hare-haren ne cikin tsari mai sarkakiya.

Ya ce ‘yan bindigar da yawansu ya kai 400, sun gudanar da ayyukansu cikin walwala ba tare da wata turjiya ba, yana mai zargin jami’an tsaron sun gaza yin aiki da bayanan da aka bayar kafin a kai harin.

Ya kuma ce babu hadin kai a tsakanin hukumomin tsaro.

A daidai wannan lokaci, Simon Lalong, wanda tsohon gwamnan jihar Filato ne, ya yi watsi da ikirarin da sojoji suka yi na cewa wajen yana da wahalar shiga kuma al’ummomin da aka kai harin sun yi nisa daga inda soja suke.

37 thoughts on “Filato: Majalisa ta gayyaci jagororin hukumomin tsaro saboda munanan hare-harem da aka kai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *