January 15, 2025

FBI ta gano wanda ya yi yunƙurin hallaka Donald Trump

1
PHOTO-2024-07-13-23-46-49.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito da sanyin safiyar Lahadin nan cewa hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta bayyana wanda ya yi yunkurin kashe tsohon shugaban kasar Donald Trump, a matsayin Thomas Matthew Crooks dan shekaru 20 a duniya.

“Hukumar FBI ta bayyana Thomas Matthew Crooks, mai shekaru 20, dan asalin Bethel Park, Pennsylvania, a matsayin wanda da ke da hannu a yunkurin kashe tsohon shugaban kasar Donald Trump a ranar 13 ga watan Yuli, a Butler, Pennsylvania,” in ji FBI a cikin wata sanarwa da NBC ta ruwaito.

1 thought on “FBI ta gano wanda ya yi yunƙurin hallaka Donald Trump

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *