December 7, 2025

Fasinjoji da Mataimakin Gwamnan Borno Sun Sha Da Ƙyar Bayan Jirgin Da Suke Ciki Ya Yi Saukar Gaggawa

images-2024-12-05T153147.617.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Umar Usman Kadafur, tare da fasinjoji fiye da 100, sun tsira daga wani hatsari lokacin da jirgin Max Air ya fuskanci matsalar inji wanda ya kama da wuta, mintuna kaɗan bayan ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Maiduguri.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 7 na yamma a ranar Laraba, lokacin da jirgin da ke kan hanyarsa zuwa Abuja ya samu tangarɗa a injinsa cikin mintuna goma bayan tashinsa.

Wannan ya sa matuƙin jirgin ya yi nasarar saukar jirgin cikin gaggawa a filin jirgin Maiduguri, inda hakan ya hana afkuwar mummunan bala’in.

Wani ma’aikacin Max Air da ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana wa manema labarai a safiyar yau Alhamis cewa: “Lokacin da jirgin ya tashi, ya yi karo da tsuntsu a sararin sama, wanda ya haddasa gobara a ɗaya daga cikin injinan jirgin. Matuƙin jirgin ya yi hanzari wajen tabbatar da tsaron fasinjoji da saukar jirgin lafiya.”

Bayan jirgin ya sauka cikin gaggawa, an ruwaito cewa fasinjojin sun shiga halin tsoro da tashin hankali, inda da yawa daga cikinsu suka zaɓi komawa gida maimakon su shiga wani jirgin.

Duk da haka, hukumar Max Air ta turo wani jirgi daga Kano domin ɗaukar sauran fasinjojin da suka yadda su yi tafiyar zuwa Abuja, ciki har da Mataimakin Gwamnan, wanda ya isa lafiya.