November 8, 2025

Fasahar Zamani: Albishir Zuwa Ga Matasa

FB_IMG_1699819522583.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

“Kar ku bari a ba ku labari”

Wannan wata dama ce ga matasa da suke da ilimi na fasahar zamani ko kuma wani karatu da za iya karantarwa ta yanar gizo.

Matashi gwanin amfani da kafar intanet da kafafen sada zumunta, Aliyu M. Ahmad ya yi rubutu game da wannan manhaja mai suna Makaranta.

Ga abin da ya rubuta:

Ɗazu da rana na yi tambaya kan, ko akwai wani ‘ILIMI’ ko ‘KWAREWA’ (skills) da za ka iya koyarwa ONLINE? Tabbas! An samu ‘responses’ da dama, abin sha’awa.

Ina mai farin cikin gabatar muku da MAKARANTA, makaranta ce ta yanar gizo kamar Udemy, Coursera, Alison, edx, Udacity… da za ka iya siyar da ‘iliminka’ ko ‘basirarka’ kan kowanne irin fanni, fahasa, kimiyya, addini, tattali, zamantakewa, adabi…a tsarin MAKARANTA cikin harshen HAUSA, har ka samu kuɗin shiga.

Makaranta za ta bawa kowa damar rijista a matsayin ‘ƊALIBI’, ko ‘MALAMI’ (INSTRUCTOR).

Ga mai son zama INSTRUCTOR, muna da kyakkyawan tsari:

1. Zai yi rijista a matsayin instructor.
2. Za mu ba shi horo na musamman kan yadda zai riƙa ƙirkirar content ya ɗorawa a shafin.
3. Akwai ‘commission’ mai tsoka ga instructor(s).

Ga duk mai son zama ƊALIBI ko INSTRUCTOR, zai iya rijista ta link dake ƙasan comment section.

Masu sha’awar kasancewa ‘INSTRUCTORS’ za su iya shiga GROUP na WHATSAPP.

MAKARANTA za ta bayyana a taron DOGARO DA KAI na ranar Lahadi 18th November, 2023 a Mambayya House, Kano. Kuma muna gina STUDIO na ɗaukar content a KANO ga masu sha’awar naɗar contents a cibiyar MAKARANTA.

A duba ‘link’ a nan: https://makaranta.ng/?fbclid=IwAR38Y4FuL6gK6gGTS-biAWKXipMNJ7rqYxKfSKAwY2LiT-oTADA494Q-uL4

#Makaranta #FasaharZamani
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari