February 10, 2025

‘Farashin Katin Waya Da Data Zai Ƙaru A Najeriya’

3
images-98.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Ministan Sadarwa, Dr. Bosun Tijani, ya bayyana cewa nan bada jimawa ba za a kara farashin katin waya da data a Najeriya.

Sai dai ya tabbatar da cewa karin ba zai kai kashi 100% kamar yadda kamfanonin sadarwa suka bukata ba.

A cewarsa, Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) za ta amince da sabon tsarin farashin kuma ta fitar da shi a hukumance nan gaba kadan.

Ministan ya bayyana bukatar samar da daidaito tsakanin kare hakkin mabukata katin waya da data da tabbatar da cewa kamfanonin sadarwa za su iya ci gaba da zuba jari a fannin.

“Muna son samar da daidaito a matsayin gwamnati don kare mutanenmu, amma kuma mu tabbatar da cewa wadannan kamfanonin za su iya ci gaba zuba jari matuka,” in ji Tijani.

“Dole ne mu tabbatar da cewa a matsayin wani fanni, mun tsara dokokin da suka dace domin habaka wannan bangare daga bangaren dokokin da muka sanya.”

Mataimakin Shugaban Hukumar NCC, Dr. Aminu Maida, ya ce hukumar ta samar da matakai don tabbatar da bin dokokin ingancin ayyuka.

3 thoughts on “‘Farashin Katin Waya Da Data Zai Ƙaru A Najeriya’

  1. Somebody essentially lend a hand to make significantly articles Id state That is the very first time I frequented your website page and up to now I surprised with the research you made to make this actual submit amazing Wonderful taskHABANERO88

  2. I do believe all the ideas youve presented for your post They are really convincing and will certainly work Nonetheless the posts are too short for novices May just you please lengthen them a little from subsequent time Thanks for the postHABANERO88

  3. I am often to blogging and i really appreciate your content. The article has really peaks my interest. I am going to bookmark your site and keep checking for new information.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *