March 28, 2025

Farashin ƙanƙara ya ninninka na burodi a Mali saboda tsananin zafi

IMG-20240430-WA0002.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Farashin ƙanƙara a ƙasar Mali ya ninninka na burodi saboda tsananin zafi da ake fama da shi.

Tun a watan Maris, yanayin zafi ya kai sama da maki 48 a wasu sassan kasar Mali, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 100 da suka hada da tsoffi da yara ƙanana.

Kusan shekara guda, da ta gabata,  kamfanin samar da lantarki na kasar Mali ya kasa samar da wadataccen hasken lantarki saboda tarin basukan miliyoyin dala a shekarun nan. Mafi akasari ‘yan kasar Mali ba su da injin jenereto saboda tsadar man fetur.

Rashin hasken lantarki ya sanya babu na’urar sanyaya daki da dare, abin da ke tilasta wa mutane kwana a waje. Hakan kuma na cutar da lafiyar mutane, kamar yadda wasu daga cikin mazauna kasar suka koka.