Fafaroma Francis Ya Rasu Yana Da Shekaru 88

Fadar Vatican ta tabbatar da rasuwar jagoran majami’ar Katolika ta duniya, Fafaroma Francis, yana da shekaru 88 a duniya.
An zabi Fafaroma Francis, wanda aka haifa da sunan Cardinal Jorge Mario Bergoglio, a matsayin shugaban cocin a shekarar 2013, bayan murabus din da Fafaroma Benedict XVI ya yi daga kan kujerar jagoranci.
Rasuwar Fafaroman ta faru ne bayan wani lokaci da ya kwashe yana fama da matsananciyar rashin lafiya.
A baya-bayan nan, ya kwana makonni a asibiti, inda likitoci suka bayyana cewa yana fama da ciwon hakarkari mai tsanani.
Tun bayan hawansa kan karagar mulki, an yi ta kallon Francis a matsayin shugaban da ke da sassaucin ra’ayi.
Ya nuna buƙatar rage tsaurin matsayar cocin kan batutuwan da suka shafi rabuwar aure da kuma auratayya tsakanin jinsi guda.
Haka kuma, ya buɗe ƙofofi na tattaunawa da shugabannin wasu addinai, duk da cewa bai sauya koyarwar cocin ta asali ba.
A zamaninsa na shugabanci, majami’ar Katolika ta fuskanci suka da dama sakamakon zarge-zargen cin zarafin yara ta hanyar lalata da ke aukuwa a sassa daban-daban na duniya.